Isa ga babban shafi

Kayan agaji sun fara isa ga fararen hula a Syria

Jiragen yakin Syria sun ci gaba da luguden wuta akan garin Douma na yankin gabashin Ghouta da ke karkashin ‘yan tawaye, jim kadan bayan da manyan motoci 13 makare da kayan agaji suka samu shiga yankin.

Wasu daga jerin manyan motocin Red Cross da na Red Crescent, dauke da kayayyakin agaji yayinda suka isa garin Douma da ke yankin Gabashin Ghouta, a Syria. 9 Maris, 2018.
Wasu daga jerin manyan motocin Red Cross da na Red Crescent, dauke da kayayyakin agaji yayinda suka isa garin Douma da ke yankin Gabashin Ghouta, a Syria. 9 Maris, 2018. REUTERS/ Bassam Khabieh
Talla

A jiya Juma’a ne kungiyar bada agaji ta Red Cross ta aike da motocin agajin biyo bayan tsagaitawar da farmakin jiragen yakin, wanda a baya ya haifar da tsaikon fara shigar da kayayyakin agajin ga fararen hula.

Akalla fararen hula dubu 400, 000 ne yaki ya rutsa da su a yankin na Gabashin Ghouta, kuma kayayyakin agajin da aka samu shigar wa yankin zai ishi taimakawa akalla fararen hula dubu 12,000 ne kawai.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce a watanni biyun farko na shekarar da muke ciki, an kai wa asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya a yankunan ‘yan tawaye hare-hare hau sau 67.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.