Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiyya ta yankewa wasu 'yan Jaridu daurin rai da rai

Kotu a Turkiyya ta zartas da hukuncin daurin rai da rai kan wasu fitattun yan jaridu 3, bisa samun su da laifin alaka da malamin addini Islaman nan Fatahullah Gulen, da ake zargi da shirya juyin mulkin kasar da da bai yi nasara ba.Muhammad Atlan da Ahama atlan wadanda yan uwan juna ne an kama su ne tun a watan Satumban bara, bayan da suka wallafa wasu labarai da ke sukar manufofin gwamnatin Shugaba Erdogan.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan. Yasin Bulbul/Presidential Palace/Handout via REUTERS
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da aka zartas da irin wannan hukunci kan yan jaridu saboda abun da mahukuntan Turkiyyar suka kira na alakar su da fitaccen malamin nan dan asali kasar wato fatahullah gulen da ke gudun hijira a Amurka, bayan da kotu ta ce ta same su da wannan laifi.

Ahamad Atlan dan shekaru 67 , wanda fitaccen marubucine kuma mamallakin jaridar Taraf ta yan adawa, da aka rufe ta, sai Muhammad Atlan dan shekaru 65, daya sha yin wallafe-wallafe kan yanayin siyasar kasar ta turkiyyar.

Baya ga wadannan akwai kuma karin wasu 'Yan jaridu da aka zartaswa makamantan hukuncin da suka hadar da tsohon manajan cinikin jaridar Zaman, wato Yakub Simsek da wasu abokan aikin sa biyu.

Tun a watan Janairu ne, kotun tsarin mulki ta bada umarnin sakin Muhammad Atlan lura da yadda aka keta masa haddi, matakin da kotun ta yi burus da shi, abunda ke jefa shakku game da bangaren shari’ar kasar, da ake kallon siyasa na taka rawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.