Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Turkiya ta musanta bude wuta kan 'yan gudun hijirar Syria

Turkiya ta musanta cewa sojojinta suna bude wuta kan ‘yan gudun hijira da ke neman ketarawa cikin kasar daga Syria.

Tankokin yakin Turkiya a kan iyakar kasar da Syria, bayan kutsawar sojojin Turkiyan yankin Afrin na Syria don murkushe mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.
Tankokin yakin Turkiya a kan iyakar kasar da Syria, bayan kutsawar sojojin Turkiyan yankin Afrin na Syria don murkushe mayakan Kurdawa na kungiyar YPG. Nazeer al-Khatib / AFP
Talla

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights watch ce ta fara fitar da rahoton a jiya Asabar, wanda ya ce dakarun Turkiya sun shafawa idanunsu toka wajen hallaka masu neman mafakar daga Syria, da ke gujewa yakin da ake gwabzawa a lardin Idlib.

Sai dai gwamnatin Turkiya ta musanta hakan, tare da jaddada cewa tun bayan barkewar yakin basasar kasar ta Syria a 2011 zuwa yanzu, Turkiyan ta bai wa ‘yan gudun hijirar Syria akalla miliyan uku da dubu dari biyar mafaka.

Hukumar kare hakkin dan adam ta 'Human Rights Watch' ta ce daga ranar 15 ga watan Disamba na shekarar 2017 zuwa 15 ga watan Janairu da ya gabata, akalla 'yan kasar Syria dubu 247 ne suka tsere zuwa yankunan da ke kan iyakar Syria da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.