Isa ga babban shafi

Turkiya na ci gaba da barin wuta a kan kurdawan Syria

Dakarun kasar Turkiya na ci gaba da barin wuta a kan kurdawan kasar Syria, inda shugaban Turkiyan ke ikirarin babu sassautawa a wannan karo.

Dakarun Turkiya na luguden wuta a Yankin Afrin na Syria kan Kurdawan YPG
Dakarun Turkiya na luguden wuta a Yankin Afrin na Syria kan Kurdawan YPG REUTERS/Osman Orsal
Talla

Tun ranar asabar din karshan mako dakarun Turkiya suka fara luguden wuta kan sansanonin Kurdawa Syria, wanda shine karo na biyu da dakarun Turkiya su ka yi kutse cikin Syria tun fara yakin kasar shekaru bakwai da suka gabata.

Jiragen sama na yaki da manyan tankunan yaki ta kasa ke ta karakaina a yankunan kasar Syria domin murkushe Kurdawan.

Ita dai Turkiya na ganin Kungiyar Kurdawa ta YPG a matsayin ‘yan ta'adda da ke samun matsuguni a yankin Afrin na Syria.

Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya ce a shirye ya ke domin ganin an gwabza wannan yaki.

Kasar Faransa dai ta nemi a yi takatsan-tsan a game da wannan rikici da ka iya zafafa rikicin Syria da ake kokarin shawo kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.