Isa ga babban shafi
Syria

Turkiya tana ci gaba da kai farmaki a Syria

Rundunar sojin Turkiya tana ci gaba da kai farmaki ta sama kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG masu samun goyon Amurka, da ke yankin Afrin a kasar Syria.

Wani jirgin yakin Turkiya yayinda ya ke keta sararin samaniyar garin Hassa wanda ke kan iyakar Turkish da Syrian a lardin Hatay. 20, Janairu, 2018.
Wani jirgin yakin Turkiya yayinda ya ke keta sararin samaniyar garin Hassa wanda ke kan iyakar Turkish da Syrian a lardin Hatay. 20, Janairu, 2018. REUTERS/Osman Orsal.
Talla

Bayan kaddamar da farmakin a ranar Juma’a, rundunar sojin Turkiyan ta ce samu nasarar kai wa cibiyoyi 108 na mayakan Kurdawan hare-hare ta sama.

A bangaren kasa kuwa sojin Turkiyan sun ce kowane lokaci daga yau zasu kaddamar da farmaki kan mayakan na YPG tare da hadin gwiwa ‘yan tawayen Syria.

Sai dai cikin sanawar da suka fitar, kakakin Kurdawan na YPG Birusk Hasaka, ya ce fararen hula 6 sun hallaka a hare-haren, yayin da wasu 13 suka jikkata.

Turkiya na kallon mayakan Kurdawan a matsayin barazana gareta, bayan daukar makamai da nufin yi mata tawaye da suka yi a shekarun baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.