Isa ga babban shafi

Afghanistan ta ce daga Pakistan ake kitsa kai mata hari

Kasar Afghanistan ta ce ta gabatarwa Pakistan wasu shaidun da ba za ta iya musantasu ba, kan yadda ake kitsa kai mata munanan hare-hare daga kasar.Batun da ke zuwa a dai-dai lokacin da al’ummah ke nuna fushinsu kan gazawar gwamnatin Afghan wajen kare rayukan fararen hula.

Matsalolin rashin tsaro na karuwa a Afghanistan
Matsalolin rashin tsaro na karuwa a Afghanistan Noorullah SHIRZADA / AFP
Talla

Harin da Afghanistan ke zargin an kitsa daga Pakistan ya hada da kazamin harin Bam din da aka kai birnin Kabul.

Amurka ta sanar da katse tallafin dala biliyan 2 da ta ke bai wa Pakistan a kokarin rabata da kungiyoyin mayakan da ta ke zargi ta na taimakawa, ciki hadda kungiyar Taliban.

Rashin tsaro a Afghanistan ya kai kololuwa, bayan harin da mayaka suka kai a gini wani shahararen Otel a birnin Kabul, da kuma wanda aka kai wa taron Jama’a da cibiyar horar da Soji a cikin makon biyu da suka gabata.

Mahukunta kasar sun daura alhakin hare-hare a kan mayakan Haqqani mai alaka da Taliban, wadda da jimmawa ake tunani na da alaka da sojin Pakistan.

Shugaban hukumar leken asirin Afghanista, Mohammad Masoom Stanekzai, ya shaidawa manema labarai cewar an gano kararar cewa an kitsa harin ne daga Pakistan da ke makwabta dasu.

Stanekzai ya ce sun bukaci Pakistan ta gabatar musu da masu hannu a hare-haren kuma sun yi musayan hujojji da ba za su musantu ba.

Sai dai Ministan cikin gidan Afghan, Wais Barmak ya ce suna kan binciken tabbatar da sahihancin bayanan da suka samu daga Pakistan.

Kabul da Amurka sun jimma suna zargin Islamabad da bai wa shugabannin Taliban da sauran kungiyoyin mayaka mafaka, zargin da Pakistan ta sha musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.