Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane 40 sun mutu a harin Kabul

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Afghanistan Waheed Majrooh ya ce wani mummunar hari da aka kai ya hallaka mutane aƙalla 40 da raunata wasu guda 70 a Kabul, babban birnin ƙasar.

Wani hari a birnin Kabul.
Wani hari a birnin Kabul. REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Tuni dai rahotanni suka ce ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakin kai harin wanda ya faru kusa da tsohon ginin ma'aikatar cikin gidan ƙasar.

Al'amarin ya faru ne mako ɗaya bayan wani harin da ƙungiyar ta ɗauki alhakin kai wa a wani otel wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutnae 18.

Mazaunan yankin sun ce sun ji ƙarar fashewar bama-bamai har sau uku.

Wani jami'in ƴan-sanda ya ce an kai harin ne a kusa da wani wurin bincike na jami'an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.