Isa ga babban shafi

Za'a murkushe mayakan IS daga Syria a watan Fabarairu - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce nan da watan Fabarairu mai zuwa, za’a kammala samun nasarar murkushe baki dayan mayakan IS a Syria.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP/Ludovic Marin
Talla

Dan haka ne Macron, ya bukaci bangaren ‘yan adawa da kuma gwamnatin kasar, da su gaggauta kokarin cimma sulhu a farkon shekara mai zuwa.

Emmanuel Macron ya bayyana hasashen ne cikin kwarin gwiwa yayin zantawar da yayi da kafar talabijin ta France 2, inda ya ce a tsakanin tsakiyar watan Fabarairun shekara mai kamawa zuwa karshensa rundunar hadaka ta kasashen ketare zata idda kakkabe ragowar mayakan IS a Syria.

Ko da yake cikin bayaninsa, Macron ya bayyana shugaban Syria Bashar al-Assad a matsayin makiyin al'ummar kasar, ya jaddada cewa ya zama tilas a tattauna da shi ko wakilansa, domin samun nasarar gaggauta sulhu tsakaninsa da ‘yan adawa.

A cewar Macron babban burin da Faransa ta sa a gaba, shi ne murkushe ragowar mayakan IS a Syria, a maimakon tilastawa Bashar Assad sauka daga shugabancin kasar kamar yadda ‘yan adawa ke bukata.

Macron ya kara da cewa, a halin yanzu babu wani wa’adi da aka diba na gaggauta ganin Assad ya sauka daga mulki bayan gamawa da mayakan IS, sai dai babu shakka wani lokaci nan gaba, dole sai shugaban na Syria ya gurfana a gaban kotun kasa da kasa, don amsa laifukan take hakkin ‘yan kasarsa da ake zarginsa da yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.