Mun kori kungiyar IS daga Iraqi- al-Abadi
Firaministan Iraqi, Haider al-Abadi ya ce an kawo karshen yakin da kasar ke yi da kungiyar jihadi ta IS, tare da ikirarin cewa dakarun kasar sun samu galaba a kan kungiyar.
Wallafawa ranar:
A wani taro a Baghdad, babban birnin kasar, al-Abadi ya ce dakarun kasar a yanzu haka su ne ke cikakken iko da iyakar kasar da Syria, saboda haka yaki ya kare.
Ya bayyana hadin kai da sadaukarwa a matsayin sirrin nasarar da kasar ta samu a kan kungiyar ta IS.
A shekara ta 2014 ne IS ta karbe iko da yankuna masu yawa a arewaci da kuma yammacin Baghdad bayan wani hari da mayakan suka kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu