Iran ta yi barazanar kara nisan zangon makamanta masu linzami
Rundunar sojin juyin juya halin kasar Iran ta yi gargadin cewa zata kara karfi da kuma nisan zangon manyan makamai masu linzamin da ta ke kerawa, da akalla kilo mita 2,000, muddin ta fuskanci wata barazana daga nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Gargadin na Iran ya zo ne bayan da kasar Faransa ta bukaci, nahiyar turai ta sake tattaunawa da Iran kan shirinta na kera manyan makai masu linzami, domin cimma yarjejeniya, bayan wadda aka cimma da kasar kan shirinta na inganta makamashin nukiliya a 2015.
Sai dai Iran ta ce tana kera manyan makamai masu linzamin ne domin kare kanta kawai, dan haka ba zata amince da duk wani yunkurin kasashen turai ba cimma yarjejeniya da ita, don ta dakatar da shirin.
A watan da ya gabata ne shugaban rundunar sojin juya juya halin Iran, Muhammad Ali Jafari, ya ce iran ta mallaki manyan makamai masu linzami da zasu iya tafiyar kilo mita 2000, abinda ke nufin zata iya amfani da su kan duk wata barazanar sojin Amurka a yankin gabas ta tsakiya, dan haka babu bukatar sai sun kara karfin nisan tafiyar da makaman zasu yi.
Iran na kan gaba a tsakanin kasashen da suka mallaki karfin manyan makamai masu linzami a gabas ta tsakiya, wanda zasu iya kai hari da su kai tsaye, kan kasar Isra’ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu