Isa ga babban shafi
Iran

Ba zamu fasa kera manyan makamai masu linzami ba - Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya ce kasar zata cigaba da kera manyan makamai masu linzami, domin kare kanta daga duk wata barazana, ba kuma zata dauki matakin a matsayin sabawa wata yarjejeniyar kasa da kasa ba.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yayin da yake gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya. 20 ga Satumba, 2017.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yayin da yake gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya. 20 ga Satumba, 2017. ©REUTERS/Stephanie Keith
Talla

Rouhani ya bayyana haka ne a yau Lahadi, yayin jawabi a kafar talabijin ta kasar.

Matsayar ta Iran ta zo ne kwanaki kadan bayanda majalisar wakilan Amurka ta amince da sake kakabawa kasar ta Iran sabbin takunkumai kan shirinta na kera manyan makamai masu linzami, don dakile yiwuwar daga likkafar kere-keren zuwa mallakar makamin nukiliya, zargin da Iran ke cigaba da musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.