Isa ga babban shafi
Iran

Zamu cigaba da kera makamai ba tare da fargaba ba - Iran

Gwamnatin Iran ta sanar da samun cikakkiyar nasara a gwajin sabon makami mai linzamin da ta yi, wanda yayi tafiyar kilomita 2,000, ta kuma ce, zata cigaba da kera sabbin makaman, domin kara karfin sojinta, duk kuwa da matsin lamba daga Amurka na ta dakatar da hakan.

wasu daga cikin sabbin makamai masu linzamin da kasar Iran ta kera.
wasu daga cikin sabbin makamai masu linzamin da kasar Iran ta kera. President.ir/Handout via REUTERS
Talla

Sakamakon gwajin makamin na jiya Asabar, Amurka ita kadai, ta dauki matakin kakabawa Iran sabbin takunkuman karya tattalin arziki, bisa hujjar gwajin ya sabawa dokar da majalisar dinkin duniya ta gindaya, na haramtawa Iran din sake yin gwaje-gwajen makamai masu linzami, da ke da alaka da kera makamin nukiliya.

Cikin sakon da ya aike da shafinsa na Twitter, shugaban Amurka Donald Trump, cewa yayi, gwajin da Iran tayi, karara ya nuna raunin yarjejeniyar da tsohuwar gwamnatin Barrack Obama ya cimma da kasar a baya, kan dakatar da shirinta mai alaka da kokarin mallakar makamin nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.