Isa ga babban shafi
Iraqi

Harin Bom din da kungiyar IS ta kai ya kashe sama da mutum 70 a Iraqi

Akalla mutane 74 ne suka rasa rayukansu akasari Iraniyawa a wani kazamin harin bom da bindiga da aka kai kusa da birnin Nasiriyah da ke kudancin Iraqi. Haka zalika da dama sun samu raunuka a harin wanda Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai farmakin a Nasiriyah na Iraqi, in da mutane 74 suku rasa rayukansu
Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai farmakin a Nasiriyah na Iraqi, in da mutane 74 suku rasa rayukansu REUTERS/Stringer
Talla

Mataimakin shugaban sashen kiwon lafiya na lardin Dhiqar da ke birnin Nasiriyah, Abdel Hussein Al-Jabri, ya shaidawa Kamfanin dilancin Labaran Faransa na AFP, cewa yanzu haka akwai sama da mutane 87 da suka samu munanan raunuka a harin bayan wadanda suka kwanta dama.

Haka kuma ya bada tabbacin cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutun ya iya karuwa nan da wani lokaci la'akari munanan raunukan da suka samu.

Al-Jabri ya kuma bayyana cewa yanzu haka zaman lafiya ya fara dawowa yankin da lamarin ya faru, baya da aka kwashe gawakin majinyatan kuma aka garzaya da su asibitoci don karbar kulawar gaggawa.

Dama dai kungiyar IS ta saba kai makamantan harin wanda ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.