Isa ga babban shafi
China

Ana fargabar mutuwar mutane 100 a China

Ana fargabar mutuwar mutane kimanin 100 sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 6.5 da ta afka wa Kudu maso Yammacin China kamar yadda alkaluman gwamnati suka nuna.

Ana fargabar mutuwar mutane 100 a wata girgizar kasa a kudu maso yammacin China
Ana fargabar mutuwar mutane 100 a wata girgizar kasa a kudu maso yammacin China REUTERS/Stringer
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Xinhua na China ya rawaito cewa, an samu asarar rayuka tare da jikkatar mutane da dama a ibtila’in girgizar kasar.

Wasu hotuna sun nuna yadda gine-gine suka rushe da suka hada da Otel a Jiuzhaigou da ke lardin Sichuan, yankin da masu yawon bude ido ke yawan ziyara, kuma ana kyautata zaton ‘yan yawon bude idon na cikin wadanda suka mutu.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawito hukumar kiyaye aukuwar bala’oi ta China na cewa, gidaje dubu 130 ne suka ruguje.

Fiye da mutane dubu 70 ne suka rasa rayukansu a wata girgizar kasa da ta taba faruwa a wannan lardi na Sichuan a shekarar 2008.

Wata mata mai suna Tang Sesheng da ke da shagon siyar da abinci a yankin ta ce, sabuwar girgizar kasar ta fi karfi fiye da wadda aka gani a 2008, yayin da jama’a suka nemi tudun- mun tsira.

Sesheng ta ce, mutane ba su ma yi tunanin daukan kaya ko kudi ba saboda kowa na ta kansa.

Shugaban kasar ta China Xi Jinping ya bukaci gagauta kai dauki ga wadanda ibtila’in ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.