Isa ga babban shafi
Iraqi-Syria

Kashe fararen hula ya karu a Iraqi da Syria

Wata Kungiya da ke Sa’ido kan rikice-rikice a duniya ta ce hare-haren da jiragen yakin kawance karkashin jagoranci Amurka ke kai wa Iraqi da Syria ya lakume rayukan fararen hula sama da 700 a watan Yuni da ya gabata.

Fararen hula da ke neman tsira a yakin Mosul na Iraqi
Fararen hula da ke neman tsira a yakin Mosul na Iraqi REUTERS/Stringer NO RESALES. NO ARCHIVE
Talla

Rahotan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amnesty international ta bukaci a aiwatar da bincike kan kisan fararen hula a lokacin da akayi kokarin kwato birnin Mosul na Iraqi.

Kungiyar Airwars da ke zaman kanta, ta ‘yan jaridu da masu bincike da ke amfani da kafafan sada zumuta da shaidun gani da ido, wajen tattara bayananta, ta ce fafatawar da akeyi da mayakan jihadi a Raqa na Syria da Mosul da ke Iraqi ya munana.

Kuma alkalluman da ta fitar ya sha ban-ban dana Amurka, da ke cewa fararen hula 603 ta kashe a bisa kuskure tun kaddamar da yakin rundunar kawance karkashin jagorancinta a 2014.

Daraktar kungiyar ta Airwars, Chris wood, ya ce karuwar hare-haren kwato Mosul da Raqa ya rubanya alkaluman fararen hula da suka kwanta dama, inda ya ce muradun Pentagon na kawar da mayakan jihadi ya jefa rayuwar fararen hula a cikin hatsari.

Kungiyar ta ce tsakanin fararen hula 529-744 aka kashe a watan Yuni, Karin sama da kashi 50 na watannin baya.

A ranar talata da ta gabata Amnesty ta bukaci a gudanar da bincike a Mosul kan kisan fararen hula, inda ta zargi dakarun Iraqi da gaza kare rayukan al’umma.

Sai dai Laftanar janar Stephen Townsend da ke jogoranci rundunar kawance yakar IS ya yi watsi da zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.