Mosul: Tsugunno bata karewa fararen hula ba
A daidai lokacin da rundunar sojin kasar Iraki ke cewa ta kama sama da kashi biyu cikin uku na birnin Mosul, wanda ake kallo a matsayin babbar cibiyar ga kungiyar ISIS ko kuma Daesh, jama’a da dama, da yakin ya rutsa da su, ke fama da matsaloli musamman a bangaren kiwon lafiya.
Wallafawa ranar:
Philippe de Vaillant, babban jami’in kungiyar agajin kiwon lafiya ta Medecins Sans Frontieres, wato kungiyar likitoci ta kasa da kasa, ya ce matsalar ta kara kamari musamman a cikin wannan wata na Yuni.
Jami’in ya ce, babban kalubalen shi ne, mutane ba sa iya isa ga cibiyoyin kiwon lafiya, musamman a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan, kuma matsalar ta fi shafar kananan yara da kuma masu manyan shekaru.
Zalika idan aka dauki jariran da ake haihuwa a ‘yan watannin nan, mafi yawansu ba su taba samun kulawar wani jami’in kiwon lafiya ba, kuma haka matsalar take a bangaren aikin tiyata, ko cire wa jama’a harsasai da dai sauransu.
A cewar Philippe de Vaillant, akwai wadanda suka share tsawon makwanni da raunuka a jikinsu, ba tare da sun samu isa ga wani jami’in kiwon lafiya domin taimaka masu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu