Saudiya ta umarci Qatar ta kwashe dabbobinta 12,000
Rakuma da Raguna sama da dubu 12 ne mallakin wasu attajirai da makiyaya ‘yan kasar Qatar, mahukuntan Saudiyya suka bukaci a kwashe daga cikin kasarta domin komawa da su Qatar.
Wallafawa ranar:
Matakin dai yana daga cikin jerin takunkuman da kasar Saudiyya da kawayenta ke ci gaba da dauka a kan Qatar bisa zargin goyon bayan ta’addanci.
Rakuman dubu 7 da kuma raguna dubu 5 sun share tsawon shekaru suna kiwo a cikin Saudiyya, kamar yadda jaridar The Peninsula da ake bugawa a Doha ta bayyana.
An dai share tsawon shekaru da attajirai da kuma sauran makiyaya ‘yan kasar ta Qatar suka mallaki filayen da aka killace, domin kiwon rakuma a sassa da dama da ke cikin Saudiyya, wadanda a yanzu aka bukaci su tattara nasu yanasu su bar kasar a cikin hanzari.
A ranar 5 ga wannan wata na Yuni, Saudiyya ta jagoranci wasu kasashen Larabawa da dama domin katse huldar diflomasiyya, kasuwanci da ma zirga-zirgar jiragen sama da kasar ta Qatar bisa zargin cewa tana goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu