Isa ga babban shafi
Indonesia

Auren-wuri- Mata sun yi taron wayar da kai a Indonesia

Mata masu da’awa a Indonesia sun gudanar wani babban taron fatawa na kwanaki uku kan matsalolin mata da ya samu halartar dubban mata daga kasashen Musulmi da dama.

Kashi 90 na Mutanen Indonesia Miliyan 255 Musulmi ne
Kashi 90 na Mutanen Indonesia Miliyan 255 Musulmi ne keywordsuggest
Talla

Matsalar auren wuri na daga cikin batutuwan da Matan suka yi fatawa akai a Indonesia mai yawan al’ummar musulmi.

Taron da aka gudanar a Yankin Java da ke Cirebon, ya kasance irinsa na farko da malamai mata suka hadu, kuma ya janyo hankali daruruwan mahalarta, yawanci daga Indonesia da Pakistan da India da Saudiya.

Matan sun yi kira ga gwamnatocin kasashen musulmi su kafa dokar aurar da ya’ya mata daga shekaru 18 sabanin 16 da ake yi yanzu haka a kasar.

Matan sun ce Hukumar kula da ilimin yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana illolin da ke tattare da aurar da mata da ba su kai shekaru 18 a duniya ba.

Kuma a cewar rahoton hukumar matsalar ta fi yawa a Indonesia, inda mata 1 cikin 4 ke aure kasa da shekaru 18.
Taron kuma ya tattauna sauran matsalolin mata da suka hada da cin zarafi da babbar matsalar gobara da ake fuskanta a Indonesia.

Yawanci Maza aka sani na bayar fatawa a Indonesia kafin wannan lokaci da mata suka fito a wani yanayi na bazata da ban mamaki don kare hakkin ‘yan uwansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.