Isa ga babban shafi
Indonesia

Musulmi ya lashe zaben gwamnan Jakarta

Wani tsohon minista a Indonesia kuma musulmi ya lashe zaben gwamnan Jakarta zagaye na biyu da aka gudanar inda ya kada gwamnan birnin mai ci kirista da ake tuhuma da yin batanci ga addinin Islama a kasar.

Sabon gwamnan birnin Jakarta Anies Baswedan.
Sabon gwamnan birnin Jakarta Anies Baswedan. © Reuters
Talla

Tuni gwamnan na Jakarta ya amsa shan kaye a zaben da aka gudanar a yau Laraba tare da mika sakon taya murnarsa ga abokin hamayyarsa Besweden da ya lashe zaben.

Basuki Tjahaja Purnama dai ya kasance gwamnan Jakarta na farko da ba musulmi ba a kusan shekaru 50 musamman a Indonesia mai yawan al’ummar musulmi, amma ya fuskanci kalubale tun a zagayen farko musamman kan zargin da ake masa a Indonesia na yin batanci ga Al Qur’ani mai tsarki.

Anies Basweden musulmi ya kada gwamnan ne da kashi 10 na yawan kuri’u, kamar yadda alkalumman sakamakon zaben suka tabbatar.

Batun batanci ga Islama ne ya ba Besweden nasarar lashe zaben zagaye na biyu a Jakarta musamman a Indonesia mai yawan al’ummar musulmi.

Besweden wanda tsohon ministan ilimi ne a Indonesia ya godewa al’ummar Jakarta da suka kada masa kuri’a har ya samu nasarar lashe zaben, tare da yin alkawalin hada kan al’ummar birrin musamman rabuwar kai da aka samu a lokacin yakin neman zabe.

Sai a watan Mayu ne dai ake sa ran tabbatar da sakamakon zaben a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.