Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane 26,000 sun tsere daga Mosul cikin kwanaki 10

Ma’aikatar lura da ‘yan gudun hijira a kasar Iraqi, ta ce mutane 26,000 ne suka tsere daga gidajensu a yammacin birnin Mosul, bayanda sojin kasar suka kaddamar da sabon farmakin kwato yammacin birnin daga karkashin kungiyar IS.  

Dakarun Iraqi yayin sabon farmakin wato yammacin birnin Mosul daga karkashin mayakan IS
Dakarun Iraqi yayin sabon farmakin wato yammacin birnin Mosul daga karkashin mayakan IS REUTERS/Stringer
Talla

Ministan ma’aikatar lura da ‘yan gudun hijirar Jassem Mohammed al-Jaff ya ce baki dayan mutanen 26,000 sun tsere ne daga yammacin birnin cikin kwanaki 10 kacal.

To sai dai hukumomin kasar ta Iraqi, sun bayyana fargabar halin da sauran fararen hular da basu iya tserewa daga yammacin Mosul din ba zasu tsinci kansu.

Gwamnatin Iraqi ta ce zuwa yanzu sama da mutane 750,000 ne har yanzu, ke karkashin mulkin mayakan IS a yammacin birnin.

A ranar 19 na watan Fabarairun da ya gabata, rundunar sojin Iraqi ta kaddamar da farmakin kwato yamacin birnin Mosul, bayan kwace gabashin birnin da ta samu nasarar yi daga karkashin mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.