Isa ga babban shafi
Iran

An yi Jana'izar Rafsanjani na Iran

Dubun-dubatan Iraniyawa ne suka yi dandazo yau talata domin jana’izar tsohon shugaban kasar Akbar Hashemi Rafsanjani, wanda ya rasu ranar lahadi yana da shekara 82 sakamakon bugun zuciya.

Jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ya jagoranci addu'ion sallar jana'izar, Marigayi Rafsanjani.
Jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ya jagoranci addu'ion sallar jana'izar, Marigayi Rafsanjani. AFP PHOTO/HO/IRANIAN SUPREME LEADER'S WEBSITE
Talla

Jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ya jagoranci addu'ion sallar jana'izar, Marigayi Rafsanjani, kan tittuna a harabar jami'ar birnin Tehran.

Akbar Hashemi Rafsanjani, shi ne ya jagoranci kasar tsakanin shekarar 1989 zuwa 1997, kuma ya kasance daya daga cikin masu fada a ji tun bayan juyin juya halin shekarar 1979 a kasar ta Iran.

Bayan Mulkinsa da ya sha suka, Rafsanjani daga bisani ya zama mai goyon bayan masu rajin kawo sauye a salon mulkin kasar.

Tun ranar Litinin Iran ta shiga zaman makokin kwanaki uku tare da daga bakaken tutoci, da alluna dauke da hotunan marigayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.