Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta hukunta mai nema wa mata hakkinsu

Wata Kotun Saudiyya ta yanke wa wani dan asalin kasar hukuncin zaman gidan yari na shekara guda bisa laifin kiran da ya yi wa masarautar kasar na bai wa mata damar walwala. 

Kasar Saudiya ita ce kadai kasar da ta haramta wa mata tukin mota a duniya
Kasar Saudiya ita ce kadai kasar da ta haramta wa mata tukin mota a duniya AFP PHOTO/FAYEZ NURELDINE
Talla

A sakon da ya aike a shafinsa na Teitter, mutumin ya ce tilastawa mata yawo da muharrami tamkar tauye musu hakki ne, lamarin da ya sa kasar ta dauki mataki a kan sa tare da cin tarar sa Riyal dubu 30.

A baya dai an samu dubban al’ummar kasar da suka sanya hannu kan wata takarda don neman kawo karshen tsarin tilasta wa mata yawo da maharrami kafin fita don gudanar da al’amuransu na yau da kullum.

Karkashin dokokin kasar Saudiya, mace ba ta da izinin yin karatu ko tafiye-tafiye ba tare da rakiyar muharraminta ba.

Kazalika, kasar ce kadai a duniya da ta haramta wa mata tukin mota, sannan kuma ta ke daukan tsauraran matakai game da walwalar mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.