Isa ga babban shafi
Philippines

Guguwa ta hallaka mutane a Philippines

Akalla mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wata guguwa mai dauke da ruwan sama da ke gudun sama da kilomita 230 a cikin awa guda da ta afka wa kasar Philippines. 

Guguwa ta hallaka mutane 4 a kasar Philippines
Guguwa ta hallaka mutane 4 a kasar Philippines Reuters/路透社
Talla

Guguwar wadda aka yi wa lakabi da Nock-Ten, ta haddasa barna ta hanyar kwashe gidaje da kuma lalata turakan wutar lantarki.

Sama da mutane dubu 218 ne aka kwashe, yayin da aka soke tashi da saukar jiragen sama gabanin aukuwar guguwar.

Philippines dai kasa ce da ta saba fuskantar irin wannan guguwa mai karfi tare da ruwan sama, in da a shekara ta 2014, wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 7.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.