Isa ga babban shafi
Iraqi

Ana fargabar mayakan ISIL za su yi garkuwa da fararen hula a Mosul

Majalisar dinkin Duniya, ta bayyana fargaba kan yiwuwar mayakan ISIL su yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, ko ma su kashe su, a kan su bari hadakar sojin Iraqi dana kasashen yamma sun ‘yanto su daga birnin Mosul.

Mayakan ISIL suna azabtar da fararen hula
Mayakan ISIL suna azabtar da fararen hula
Talla

Shugaban sashin kula da kare hakkin dan’adam na Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad al Hussain, ya ce sun da rahotanni da ke cewa, mayakan na ISIL sun tilastawa iyalai 200 daga kauyen Samalia da ke kusa da Mosul shiga cikin birnin.

Yayinda mayakan suka sake tilastawa wasu iyalan 350 daga kauyen Najafia shiga cikin birnin na Mosul, dai dai lokacin da sojin Iraqi, ke dada matsar tungar karshe ta ISIL mafi karfi a kasar.

Kakakin sashin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards ya ce sama da fararen hula 3,900 aka raba da gidajensu a birnin na Mosul, sakamakon kazamin fadan da ake gwabzawa a birnin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.