Isa ga babban shafi
China

China ta kaddamar da na'urar gano bayanai kan sararin samaniya

Kasar China ta kaddamar da fara aikin wani katafaren madubin bincike a kudu maso yammacin kasar, wanda masana kimiyya a kasar suka zai taimaka wajen gano ko akwai wasu al’ummomin da ke rayuwa a wasu Duniyoyin na daban.

NASA
Talla

Na’urar da aka kashewa kudi dala miliyan 180, tana da kwatankwacin fadin filayen wasan kwallon kafa 30.

Masana a China sun kwashe akalla shekaru 19, suna bincike da aikin kera wannan Na'urar bincike kafin kaddamar da ita.

Ana sa ran wannan yunkuri na China, ya saka ta zama kan gaba wajen bincike sararin samaniya tsakanin kasashen duniya nan da shekaru 10 zuwa 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.