Isa ga babban shafi
Syria

Za a fara kwashe fararen hula a Daraya

Motocin kungiyar agaji ta Red Crescent sun shiga yankin Daraya domin kwashe dubban fararen hula da ‘Yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria suka yi wa kawanya bayan cim ma yarjejeniyar kwashe su daga yankin da ke kusa da Damascus.

Za a kwashe mutanen Daraya a Syria
Za a kwashe mutanen Daraya a Syria Fadi Dirani / AFP
Talla

An shafe tsawon shekaru hudu dakarun gwamnati na kewaye da garin Darayya tun a 2012.

Yanzu kuma gwamnatin Syria da ke shirin karbar ikon garin ta amince a kwashe fararen hula da ‘Yan tawaye wadanda aka kiyasta sun kai sama da 8,000.

Dubban mutanen Daraya na fama da matsalar katsewar abinci da ruwan sha sakamakon hare haren dakarun gwamnatin Syria.

Rahotanni sun ce ‘Yan tawaye sun mika makamansu ga Dakarun Gwamnati domin samun damar ficewa yankin na Daraya.

Wannan dai na nufin dakarun gwamnati sun samu galaba akan ‘Yan tawayen.

Daraya na cikin yankunan da aka fara zanga-zangar adawa da mulkin shugaba Bashar al Assad a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.