Isa ga babban shafi
India

Ambaliya ta lalata gidaje miliyan daya a India

Jami`an ceto a India sun ce sama da mutane 152 ne suka rasa rayukansu sakamakon cigaba da saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya fara makwanni uku da suka gabata, wanda ya jawo ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa a West Bengal-India
Ambaliyar ruwa a West Bengal-India REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

Jami`an ceton sun ce a arewa maso gabashin jihar Assam kadai mutane 34 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan, yayinda mutane miliyan daya da dubu dari suka rasa gidajensu.

Ma`aikatan ceto a kasar India na kokarin kwashe wasu dabbobi da ambaliyar ruwan ta ritsa da su a gidan ajiye dabbobi na Kaziranga dake jihar ta Assam, inda sama da dabbobin dari suka mutu saboda ambaliyar.

Rahotanni sun ce ambaliyar ruwan ta kuma lalata maka makan filayen noma a jihohin Bihar da Himachal Pradesh a arewacin kasar ta India sai kuma jihar West Bengal dake gabashin kasar.

Hukumar hasashen yanayi ta kasar india ta ce akwai kyakkyawan zaton cigaba da saukar mamakon ruwan saman a kwanaki masu zuwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.