Isa ga babban shafi
Asia

Ruwan sama mai tafe da iska ya kashe dubban mutane a yankin Asiya

Ruwan sama mai tafe da iska ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a wasu kasashe na yankin Asiya da suka hada da India da Pakistan da Myanmar.Matsalar ta haifar da ambaliyar ruwa da kuma zabtarewar kasa.

Photo : AFP
Talla

Mahukuntan India sun ce kimanin mutane 120 suka mutu a sassan kasar da ambaliyar ruwan ta shafa yayin da sama da miliyan suka rasa gidajensu a tsawon mako guda da aka yi  ana tafka ruwan sama.

A yau Litinin Jamai’an agaji sun shiga kauyukan da matsalar ta shafa a lardin Manipur.

A kasar Myanmar ma akalla mutane 46 aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da matsalar ta ambaliyar ruwa ta shafi sama da mutane dubu dari biyu.

Ruwan sama mai tafe da iska ya yi sanadin rusa gidaje sama da 700 a jihar Hakha na Myanmar, tare da lalata yammacin Jihar Rkhine da ke yankin ‘Yan kabilar Rohingya musulmai.

Yanzu haka kuma mahukuntan kasar na kokarin kai dauki tare da taimakawa wadanda matsalar ta shafa.

Haka ma dai matsalar ambaliyar ta shafi Pakistan domin kimanin mutane 116 suka mutu kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.