Isa ga babban shafi
INDIA

Masu zanga zanga 5 sun mutu a India

Mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu a arangama tsakanin masu zanga zanga da sojin gwamnati a yankin Kashmir sakamakon kisan da aka yiwa wani madugun adawa.

Talla

Akalla mutane 23 ne suka mutu tun bayan soma zanga zangar a ranar juma’ar da ta gabata, a yayin da wasu daruruwa suka sami rauni, duk kuwa da dokar hana fita da gwamnati ta ayyana a yankin.

Yanzu haka ma dai al’ammura sun tsaya cak sanadiyar rikicin, wannan ya kasance tashin hankali mafi muni da yankin ke fuskanta tun shekarar 2010.

A ranar juma’ar da ta gabata ne aka soma zanga zangar bayan kisan da aka yiwa madugun adawa kuma jagoran kungiyar Hizbul Mujahideen na yankin Kashmir a arangamar da ta auku tsakanin magoyansa da dakarun gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.