Isa ga babban shafi
India

Mutane 17 sun mutu a cibiyar aje makami a India

Wata gobara da ta tashi a rumbun aje makaman sojin kasar India ta yi sanadiyar rasa rayukan mutane 17, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi Reuters/Rob Stothard/Pool
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce cikin mutane 17 da suka mutu sun hada da sojoji 2 a tashar Pulgaon da ke kusa da birnin Nagpur a Jihar Maharashtra.

Tuni aka kwashe dubban mutanen da ke zama a kauyukan dake kusa da tashar domin fargabar sake fashewar wasu abubuwa.

Rahotanni sun ce an yi kokarin kashe gobarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.