Mutane 500 sun mutu a Syria
A kasar Syria, mutane sama da 500 aka tabbatar da mutuwarsu a cikin wannan watan na Fabairu kadai, hakan kuwa ya faru ne sakamakon luguden wutan da dakarun gwamnatin kasar ke yi kan ‘yan tawaye tare da samun goyon bayan Rasha .
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar da ke sa ido kan rikicin Syria ta tabbatar da mutuwar mutane dari biyar da shida a yankin Aleppo, sakamakon munanan hare haren da dakarun gwamnati suka kaddamar a mabuyar 'yan tawayen a farkon wannan watan.
Asarar rai da aka tafka ta kara haddasa matsalar tserewar dubban mutane daga kasar zuwa kan iyakar Turkiya, yayin da Turkiyan ta ki ba su damar shiga kasar saboda tana fama da 'yan gudun hijrar Syria sama da miliyan biyu a yanzu haka.
Hare haren Rasha a Syria dai na ci gaba da fuskantar suka daga wasu kasashen duniya yayin da majalisar dinkin duniya ta yi kira ga Rasha da ta gaggauta kawo karshen hare harenta a Syria ganin asarar rayukan fararen hula da ake samu a duk lokacin da ta yi luguden wuta da zummar tarwatsa masu tada kayar baya.
Sama da shekaru hudu da barkewar yakin basasa a Syria amma har yanzu rikici na ci gaba da ruruwa.
A makon da ya gabata ne aka sake dage zaman sulhu da aka shirya yi bisa dalilai na kasa samun hadin kai tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu