Isa ga babban shafi
Syria

Mutane sun mutu a harin asibitin Syria- MSF

Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier ta ce wani harin sama da aka kai asibitin da ta ke taimakawa a kasar Syria ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 da kuma raunana wasu guda 6.

Shugaban kungiyar Medicin Sans Frontier Mego Terzian.
Shugaban kungiyar Medicin Sans Frontier Mego Terzian. RFI
Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar ta nuna cewar an kai harin ne a ranar 5 ga wannan wata na Fabairu a garin da ke da nisar kilomita 12 daga iyakar kasar da Jordan, kuma cikin wadanda aka kashe har da wata mai taimakawa likita.

Wannan shi ne karo na uku da ake kai hari asibiti a kasar abinda yayi sanadiyar lalata asibitoci 177 da kuma hallaka ma’aikatan lafiiya kusan 700.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.