Isa ga babban shafi

‘Yan majalisun Isra’ila sun kada Kuri’ar dokar dauri kan Falasdinawa

‘Yan Majalisar kasar Isra’ila sun kada kuri’ar amincewa da dokar daurin shekaru uku a gidan yari a kan Falasdinawa da ke jifar yahudawa da duwatsu.Daukar matakin na zuwa ne bayan Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya sha alwashin daukar tsauraran matakai a kan masu jifa da duwatsu.

Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel.
Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

A yammacin Jiya ne Majalisar Isra’ila ta amince da kudirin dokar, kuma ‘Yan majalisa 57 ne suka amince yayin da 17 suka kada kuri’ar kin amincewa.

An amince da dokar ne dai bayan Firamnistan Isra’ila ya bayyana kaddamar da yaki da masu jifa da duwatsu, yayin da aka shafe sama da wata guda ana rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan.

Majalisar dai ta amince ne da matakin daurin shekaru uku akan duk wanda aka kama da lafin jifa da duwatsu. Wanda hakan ke nuna dokar za ta yi matukar tasiri a kan Falasdinawa musamman matasa da ke jifar jami’ar tsaron Isra’ila.

‘Yan majalisa dai masu ra’ayi iri guda, da na Netenyahu sun ce amincewa da dokar ya zama wajibi domin maganin wadanda ke jifar mutane, musamman bayan mutuwar wani Bayahude dan shekaru 67 da yi hatsari da mota sakamakon jifan shi da duwastu kamar yadda ‘Yan sandan Isra’ila suka bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.