Isa ga babban shafi
MSF-KUNDUS

MSF ta karrama ma’aikatanta da aka hallaka a Kunduz

Kungiyar likitoci ta MSF ta karrama wasu ma’aikatanta da suka rasa rayukansu sakamakon harin Amurka da ya ritsa da asibitinta da ke birnin Kunduz na Afghanistan.Sama da mutane 250 ne suka hallarci bikin Karramawar da akayi a birnin Geneva.

Shugabar Kungiyar MSF Joanne Liun
Shugabar Kungiyar MSF Joanne Liun REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Kallaman daina kai hare-hare a kan asibitoci, shine kira da kungiyar ta yi yayin karrama ma’aikatan da harin da Amurka ta ce, ta kai bisa kuskure ya ritsa dasu a Afghanistan a farkon watan da ya gabata.

Shugabar kungiyar Joanne Liu ta yi gargadi cewa ba da gaskiyar cikakken bayyani kan yadda wannan hari ya auku a Kunduz, shine hanyar da zai iya kare aukuwar kwatan-kwacin haka a gaba.

Inda kuma ta ce a garesu ya zama dole su dau matakan kwato hakin su, domin ya zama darasi a gaba da kuma kare rayukan fararan hula.

Masu bincike karkashin jagoranci Amurka, NATO da hukumomin Afghanistan na cigaba da binciken wannan hari da ya hallaka mutane 30, sai dai bukatar MSF ita ce bincike ya koma karkashin jagoranci kungiyar mai zaman kanta domin Kungiyar na gani cewa Amurka za ta boye gaskiya.

Sama da mutane 250 ne suka hallarcin bikin karramawar dauke da alluna da ke rubuce da a gudanar da adalci, a binciken kisan Jami’an MSF domin a yanke musu hukunci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.