Isa ga babban shafi
Isra'ila

Rikici ya tsananta a birnin Kudus

Rikicin sama da mako guda tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a birnin kudus ya ta’azara har zuwa yankin Gaza, bayan harbe mutane 5 da Jami’an tsaron Isra’ila suka yi, abinda ya sa Kungiyar Hamas yin kira na gudanar da Intifada.

Rikici ya tsananta a birnin Kudus.
Rikici ya tsananta a birnin Kudus. REUTERS/Mohamad Torokman
Talla

Sabon rikicin ya barke ne bayan Shugaban Hamas a lokacin hudubar sallar Juma’a ya umarci a fito domin gudanar da Intifadar neman yanci kai.

Mai magana a madadin dakarun, ta ce sama da Falasdinawa 200 ke gudanar da tarzomar inda suke amfani da manyan duwatsu da tayoyi wajen afkawa jami’an tsrao Isra’ila.

Yayin da wasu rahotannin ke cewa dakarun Isra’ila sun bude wuta kan matasa da ke jifansu, abinda ya yi sanadiyar mutuwar Masatan Falasdinawa 4 da basu haura shekaru 20 ba tare da jikata wasu 21.

A halin yanzu a yankin Gaza rikicin ya tsananata bayan daba wa wasu Falasdinawa wuka da Yahudawan Isra’ila suka yi.

Hakulan duniya sun karkata kan wannan rikicin da ka iya haifar da intifada a karo na uku, bayan na shekarar 1987 da 2000.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.