Isa ga babban shafi
Malaysia

Addu'a ga mutane da suka mutu cikin jirgin da aka harbo a kasar Ukraine

‘Yan uwan mutanen da suka rasa ransu cikin jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH17, da aka harbo cikin shekarar bara, a sararin samaniyan kasar Ukraine na neman a musu adalci kan batun. Mutanen sun yi wannan kiran ne Yau Asabar, lokacin da shirin adu’ar cika shekara guda da aukuwar lamarin. 

Gawar daya daga cikin mamatan jirgi mai lamba MH 17 na kasar Malaysia
Gawar daya daga cikin mamatan jirgi mai lamba MH 17 na kasar Malaysia REUTERS/Olivia Harris
Talla

Fraiministan kasar ta Malaysia Najib Razak ya halarci bukin addu’ar, da aka gudanar a babban filin jirgin saman birnin Kuala Lumpur, inda dangin mamatan suka bayyana yadda ake jan kafa wajen gudanar da bincike kan lamarin.
Sun bayyana bukatar ganin an gano wanda ya harbo jirgin saman, da ya taso daga birnin Amsterdam na kasar Nethrlands ya nufi Kuala Lumpur din kasar Malaysia, inda dukkan Pasinjoji 298 dake ciki suka mutu.
Ana zargin ‘yan awaren kasar ta Ukraine da amfani da makaman kakkabo jirage, wajen harbon jirgin.
Ana gudanar da taron addu’o’in ne a yau Asabar, mai makon ranar 17 ga watan nan, da zata kasance ranar Sallar Idil Fitri, da ake yi a karshen watan Ramadan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.