Ramadan: Dubban Musulmai sun yi sallar Jumma'a a birnin Kudus
Dubban musulmai ne suka gudanar da sallar Jumma’a a masallacin Baitul Mukaddis bayan sassauta matakan shiga masallacin da Isra ‘ila ta yi a yau albarkacin watan Ramadan.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘yan sanda sun ce, kimanin musulamai dubu 80 ne daga birnin Kudus da yammacin kogin Jordan kadai suka halarci masallacin.
A bangare guda, Sheik Azzam Al-Khatib, Shugaban kwaminitin musulmai deke kula da masallacin ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, a kiyasce, masallata dubu 200 ne suka taru a ciki da kewayen masallacin.
Kafin wannan ranar ta jumm’ar farkon Ramadan, ba kasafai ake barin musulmai shiga masallacin ba musamman matasa 'yan kasa da shekaru 40 saboda gudun tayar da tarzoma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu