Isa ga babban shafi
Iraqi-syria

Sojin kawance sun kai hari kan IS domin kare Alqa'ida

Karon farko tun daga lokacin da suka soma kai farmaki ta sama a cikin kasashen Iraki da Syria, sojojin kawance karkashin jagorancin Amurka sun kai farmaki kan mayakan IS da ke kokarin shiga yankin Alep da ke hannun ‘yan Alqaida.

Sojoji a yankin Alep na Syria
Sojoji a yankin Alep na Syria REUTERS/Mohamad Bayoush
Talla

An dai share tsawon mako daya mayakan na IS na fatattakar mayakan na Alqaida a cikin Syria, kuma hare-haren da jiragen yakin kawance suka kai na a matsayin kariya ga mayakan na Alqaida a cewar manazarta al’amurran da ke faruwa a yakin.

Jiragen saman sojojin kawancen dai sun kai hari har sau hudu, lamarin da ya tilasta wa mayakan masu da’awar jihadi dakatar da yunkurinsu na kama garuruwan Mareh da kuma Aazaz da ke hannun ‘yan Alqaida.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.