Isa ga babban shafi
Syria

Rundunar kawance ta kashe fararan hula a Syria

Hare haren da rundunar kawance ta ke  kai wa karkashin jagorancin Amurka ta yi  sanadiyar mutuwar ma’aurata da ‘ya‘yansu biyar, kamar yadda kungiyar dake sa ido a kan Syria ta bayyana a ranar litinin

Suran Jiragen sama dake kai hare hare a Syria
Suran Jiragen sama dake kai hare hare a Syria
Talla

Kungiyar dake da cibiya a birtaniya ta ce, an kashe ma’auratan ne da yaransu a kauyan Daly Hassan dake arewacin birnin Aleppo kuma kawo yanzu fararan hula 148 ne suka rasa rayukansu kama daga lokacin da dakarun kawancen suka fara kai farmaki kan mayakan IS a watan Satumban bara a Syria.

A cewar kungiyar, akasarin wadanda harin ya cika da su mata ne da kananan yara kamar dai yadda ya taba faruwa a watan daya gabata a kauyen Birmahle dake Aleppo, inda farmakin dakarun ya kashe fararran hula 64 kuma rabinsu kananan yara ne.

A bangare kuda, ma’aikatar tsaron Amurka ta musanta cewa rundunar kawancen da Kasar ke jagoranta ta kashe fararan hula a Syria duk da rahotanni da dama da aka fitar kan wannan batun na kisan fararan hula da basu ji basu gani ba.

Kimanin mutane dubu 220 ne suka mutu tun lokacin barkewar tarzoma a kasar ta Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.