Isa ga babban shafi
Kuwait

Ana ci gaba da samun karuwar rashin aikin yi a kasashen Larabawa

Hukumar kwadagon kasashen larabawa tace, kashi 30 cikin 100 na matasa da ke kasashen larabawa na fama da rashin ayukan yi. A lokacin da yake Jawabi a wani taron kasashen larabawa na kwanaki 5 da ake gudanarwa a kasar Kuwait, Darakta Janar Na hukumar kwadago yankin kasashen larabawa, Ahmed Muhammad Luqman ya ce rashin kwanciyar hankali da kuma karancin masu zuba jari, sun tilastawa matasa musamman wadanda basu haura shekaru 30 ba, fama da rashin ayukan yi a yankin.Ahmed Luqman ya kuma bayyana yadda wadanda suka kammala Jami’o’i ke rasa ayukan yi a ma’aikatun da ke cewa basa bukatar su.Rahotannin dai na cewa daga shekarar ta 2011 zuwa yanzu akalla an samu matasa miliyan 2 marasa ayukan yi, lamarin da yasa a yanzu ake da yawan adaddin matasa miliyan 20 a yankin larabawa dake fama da rashin abin yi.Ahmed Luqman yace wannan adadin, ya ninka abinda ake dashi a kasashen duniya har sau 3.A wanin hasashen, hukumar ta bayyana cewar, alkalluman rashin ayukan yi zasu karu cikin wannan shekarar da kuma badi, Lamarin da daraktar Janar a hukumar kwadago ta duniya Guy Ryder ke gargadi cewar babbar barazana ce ga zaman lafiya a yankuna larabawa Baki daya. 

Sakatare Janar na kungiyar kasashen Larabawa, Nabil al-Arabi
Sakatare Janar na kungiyar kasashen Larabawa, Nabil al-Arabi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.