Isa ga babban shafi
Pakistan

A karon farko cikin shekaru 7, Sojin Pakistan sun yi Atisaye

A karo na farko cikin shekaru 7, Sojin Kasar Pakistan sun gudanar da Atisaye a bikin ranar samun yan cin kai, dan nuna karfin da kasar ke da shi na yakar Kungiyar Taliban

Raheel Sharif, Shugaban Sojin Pakistan
Raheel Sharif, Shugaban Sojin Pakistan Reuters
Talla

An gudanar da Atisayen ne a Islamabad, babban birnin kasar, bayan katse hanyar sadawar ta wayar Salula a duk fadin birnin, tare da hana zirga zirgar ababan hawa a wasu bangarori, dan hana kaddamar da harin bama bamai, yayinda kuma, jami’an tsaro suka bazu ko ina saboda tabbatar da cikkaken tsaro ga Sojin dake Atisayen.

Tun a shekarar 2008, raban Kasar da ta gudanar da irin wannan Atisayen, bayan hukumomin kasar sun dakatar da yin sa, sakamakon dari darin farmakin da mayakan Taliban kan iya kaddamarwa Sojin, a lokacin gudanar da bikin.

Taron Atisayen, ya samu halartar Shugaban Kasar, Mamnoon Hussain, da Firaministan, Nawaz Shariff, da kuma Raheel Sharif, shugaban Sojin Kasar.

A dayan bangaren, Atisayen bikin ranar samun yan cin kan na zuwa ne,, watanni uku da mutuwar mutane 150, a wani hari da Kungiyar Taliban ta kaiwa wata makaranta dake birinin Peshawar, lamarin da ya tada hankulan hukumomin kasar, lura da cewa, kananan yara ne harin ya fi cika wa da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.