Isa ga babban shafi
Pakistan

Kungiyoyin Mayakan Pakistan uku sun hade

Wasu manyan kungiyoyin da ke dauke da makamai a yankin arewa maso yammacin kasar Pakistan su uku, sun yanke shawarar hadewa waje guda, domin samun karfin tunkarar dakarun sojan kasar da ke ci gaba da yi ma su balbalin wuta a yankuna da dama na kasar ta Pakistan.

Mayakan Taliban
Mayakan Taliban AFP PHOTO / Noorullah Shirzada
Talla

Yanzu haka dakarun kasar Pakistan sun kara rubbanya hare haren da suke kai wa kungiyoyin mayakan da kuma ‘yan tsagera da ke dauke da makamai da Mayakan Taliban da suka kai wani harin ta’addanci da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 da suka hada da kananan yara a wata makaranta da ke yankin Peshawar a cikin watan Disemban da ya gabata.

Kungiyar Taliban ta Jamat-ul-Ahrar da kuma mayakan kungiyar Lashkar-e-Islam da Tehreek-e-Taliban (TTP), ne suka hade a waje guda domin tunkarar farmakin da dakarun gwamnatin ke kai masu ba tare da kakkautawa ba.

Kungiya TTP da Mollah Fazlullah, ke jagoranta ita ce ta dauki harin 2012 da aka kai a kan dalibai ‘yan makaranta da ya yi sanadiyar yi wa Malala Yousefzai, dalibar nan da aka bai wa lambar yabo ta Nobel mummunan rauni.

Tun bayan mummunan harin da kungiyar Taliban ta kai a filin sauka da tashin jiragen saman birnin karachi wanda ya yi sanadiyar hasarar darurukan rayukan fararen hula ne gwamnatin kasar ta Pakistan ta daura damarar yaki da kungiyoyin da ke dauke da makamai da suke kokarin durkusar da kasar tamkar makwabciyarta kasar Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.