Isa ga babban shafi
Vanuatu

An bukaci kasashen duniya su taimaka wa al'ummar Vanuatu

AN zargi kasashen duniyar dake da arziki da kaucewa daukar nauyin da Allah ya dora musu na taimakawa kasashen da bala’i ya shafa.Wanan suka na zuwa ne a wajen wani taron kasahsen duniya da ake yi yanzu haka a Sendai dake kasar Japan wanda kasashe 190 ke halarta.Taron ya kawo misali da abinda ya faru a Vanuatu wanda yanzu haka ke fama da matsalar rashin abinci da ruwan sha amma kasashen dake da kumbar susa sun kauda kan su daga batun.A wani bangaren kuma, an soma samun saukar kayan agaji a Vanuatu, tsibirin da ya gamu da bala’in iska da ruwan sama a karshen mako, sai dai kamar yadda rahotanni ke cewa akwai wasu bangarorin acikin kasar da al’umma ke cikin matsanancin hali na rayuwaAn fara isar da kayayyakin agajin jinkai daga wasu kasashen duniya a tsibirin Vanatu dake tekun Pacific da guguwar Pam ta share a ranar juma’ar da ta gabata. kungiyar bayar da agaji ta Oxfam tare da kasar New Zealand sun isar da kayayyakin agajin gaggawa duk da koma bayan da kungiyoyin ke fuskanta na rashin hanyoyin mota wajen isar da agajin.An dai bayyana cewa yanzu haka akwai wasu sassan a kasar da jami’an agajin suka kasa kai dauki, sakamakon rashin hanyoyin.Wani hoton tauraron dan Adam ya nuno jama’ar yankunan Ambryn da Tongoa na bayyana bukatunsu a rubuce ganin babu hanyoyin da taimakon zai kai garesu,Ana sa ran a yau alkhamis a samun karin agajin daga wasu kasashen na duniya da katafaren kamfanin nan mai samar da man kwakwa na COPSL ya dauki nauyin saukewa.Tsibirin Vanuatu dai dake kudancin tekun Pacific a ranar juma’ar da ta gabata ne ya fuskanci mahaukaciyar Guguwar da aka yiwa lakabi da suna Pam dake tafe da ruwan sama mai karfi, da suka haddasa barnar da bata misiltuwa inda aka bayyana cewa, kusan kashi 90 cikin dari na fadin tsibirin mai kunshe da mutane dubu 270 ya zama fili.  

Irin ta'adin da guguwar Pam tayi a yankin Port Villa, na kasar Vanuatu
Irin ta'adin da guguwar Pam tayi a yankin Port Villa, na kasar Vanuatu Reuters/Dave Hunt/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.