Isa ga babban shafi
Falasdinawa

Falasdinawa za su kalubalanci Isra’ila a ICC

A karon Farko, Falasdinawa sun ce za su shigar da kara a kotun ICC a ranar 1 ga watan Afrilu domin kalubalantar ta’asar da Isra’ila ta aikata na laifukan yaki a Gaza da kuma mamayar yankunansu.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Mike Segar
Talla

Kungiyar fafutikar samun ‘yancin Falasdinawa ta PLO tace a ranar 1 ga watan Afrilu ne zata shigar da kara domin kalubalanatar ta’asar da Isra’ila ta aikata a Gaza, kamar yadda wani mamba a kungiyar ya tabbatarwa kamfanin dilllacin labaran Faransa.

Wannan na zuwa ne bayan sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya tabbatar da cewa a ranar 1 ga watan Afrilu mai zuwa za a tabbatar da wakilcin Falasdinawa a kotun ICC, wanda hakan kuma zai ba su damar kalubalantar Isra’ila a kotun.

A ranar 16 ga watan Janairu ne Kotun ICC ta kaddamar da binciken barnar da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa musamman rikicin watan Afrilun bara inda Falasinawa kimanin 2,200 suka mutu.

Tun bayyana matakin samun wakilcin na Falasdinawa, Isra’ila ke daukar matakan martani na datse kudaden harajin da ta ke karba a madadin gwamnatin Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.