Isa ga babban shafi
ICC

ICC ta ce ba zata tuhumi Isra’ila akan kai hari wa Jirgin Ruwan masu agaji a 2010 ba

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta Duniya ICC ta ce ba za ta tuhumi kasar Israila ba, dangane da hari da ta kai akan jirgin ruwan masu bada agaji a yankin kan iyakar Tekun Gaza a cikin shekara ta 2010 ba, hari da yayi sanadi mutuwa ‘yan kasar Turkiya akalla 10

General view of the ASEAN Plus Three Foreign Ministers' Meeting at Myanmar International Convention Centre (MICC) in Naypyidaw, August 9, 2014. REUTERS/ Soe Zeya Tun (MYANMAR - Tags: POLITICS)
General view of the ASEAN Plus Three Foreign Ministers' Meeting at Myanmar International Convention Centre (MICC) in Naypyidaw, August 9, 2014. REUTERS/ Soe Zeya Tun (MYANMAR - Tags: POLITICS) Reuters/路透社
Talla

Babbar mai gabatar da kara a Fatou Bensouda ta ce ba za’a gudanar da wani bincike ba ko gabatar da tuhuma akan wanna hari, wanda ya yi sanadi mutuwar fararen Hula 10, kasancewa babu kwararan hujoji.

Fatou ta ce shaidu da aka gabatar bai gamsar da ita cewar Isra’ila ta kai wannan hari akan Jiragen ruwa ba, kuma kotu ba zata iya daukar wani mataki ba kan gurfanar da wadanda ake zargi.

Akala ‘yan kasar Turkiyya 9 ne suka mutu a lokacin da Dakarun kasar Isra’ila suka kaddamar da hari kan jerin gwanon Jiragen ruwan agaji, yayin da Dakarun Israilar ke kokarin rufe yankin kan iyakar ruwa da ke a yankin Gaza a ranar 31 ga watan mayu.

A cikin shekarar ta 2012 wata kotu a kasar Turkiya, ta umarci a kamo tsofaffin shugabanin sojin kasar Israila hudu wadanda ake zargi da hannu wajen kai hari, a lokaci da kungiyoyin agaji da Iyalan wadanda suka rasa rayukansu, suka shigar da kara,
wanda hakan bai samu ba, illa haifar da rikicin huldar Diplomasiyya tsakanin kasashe guda biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.