Isa ga babban shafi
Isra'ila-Felesdinu

Hamas tace ta’adin Isra’ila a Gaza ya haura kudi euro Biliyan

Kungiyar Hamas ta yi zargin cewar harin da Israila ta kwashe kwanaki Takwas tana kai wa a Gaza, ya yi ta’adin da ya kai kudi euro Biliyan daya da Miliyan Dari Biyu, bayan kisan fararen hula 166 da rusa gidaje 200 da lalata wasu gidajen 8,000, tare da Masallatai uku da asibiti.

Wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza
Wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza REUTERS/Mohammed Salem
Talla

Ahmad yusuf, mai bai wa Firaminista, Ismaila Haniya shawara, yace za su ci gaba da mutunta tsagaita wuta, muddin Israila ba ta karya yarjejeniyar ba.

A lokacin da Isra’ila ke kai hare hare, Dakarun Sojin kasar sun ce suna kai hare hare ta sama da 1,500 da wasu hare hare kuma da aka kai ta karkashin kasa.

Wasu Alkalumma da ma’aikatar Lafiya ta fitar a Falesdinu ya nuna tsakanin ranar 14 zuwa ranar 21 ga Watan Nuwamba, Falesdinawa 166 suka mutu a Gaza yawancinsu fararen hula kuma wasu mutanen 1,235 ne suka samu rauni a jerin hare haren da Isra’ila ta kai.

A hare haren Rokoki da Hamas ta kai zuwa Isra’ila an ruwaito mutane Shida ne kacal suka mutu, hudu daga cikin fafaren hula biyu kuma Sojin Isra’ila amma mutane 240 ne suka jikkata kamar yadda Rundunar Sojin Isra’ila ta tabbatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.