Abudlkader Mullah zai fuskanci hukunci kisa a Bangladesh
Kotun kolin kasar Bangladesh, a yau alhamis ta tabbatar da hukuncin kisan da wata kotun ta yankewa daya daga cikin shugabannin jam’iyyar Jama’ati Islami Abudlkader Mullah, saboda samun sa da laifin kashe jama’a a lokacin gwagwarmayar samawa kasar ‘yanci a shekarar 1971.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mullah ya shigar da kara ne a gaban kotun kolin inda ya ke neman a soke umurnin zartas ma sa da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa da wata kotun ta yanke masa a can baya.
A watan Fabrairu ne kotu ta yanke hukuncin samun Mullah da laifin aikata laifukan yaki a lokacin neman ‘Yanci daga Pakistan.
Tuni Mullah daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ya musanta zargin da ake masa.
Akwai shugabannin Jam’iyyar da dama da aka yanke wa hukunci, al’amarin da ya haifar da zanga-zanga daga magoya bayan Jam’iyyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu