Kotu ta yanke hukuncin kisa kan sojoji 150 a kasar Bangladesh
Babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Bangladeshe Baharul Islam, ya ce ko shakka babu wadannan sojoji 150, na da hannu dumu-dumu wajen kashe manyan jami’an sojan kasar a lokacin wannan bore.
Wallafawa ranar:
A jimilce dai sojoji 350 ne kotun ta sama da laifi daga cikin 823 da aka gurfanar a gabanta, kuma an yanke masu hukuncin dauri da ya kama daga shekaru 4 zuwa 14 a gidan yari.
Masu boren dai sun balle rumbun ajiye makamai sannan suka dauke bindigogi dubu 2 da 500, kafin daga bisani su afka wa wani gini da manyan jami’an sojan kasar ke gudanar da taro, inda a can ne suka kashe 57 daga cikinsu bayan sun dan yi garkuwa da su na gajeren lokaci a ranar 25 ga watan fabarairun 2009 suna neman a kara masu albashi.
Har ila yau bayan sun kashe mutanen, masu bore sun jefa gawarwakinsu a cikin ramuka da kuma magudanan ruwa. Wannan ne dai boren soja mafi muni da kasar ta taba fuskanta a cikin tarihinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu