Isa ga babban shafi
China

An cafke Mutane 1000 a China masu yada fatawar karshen Duniya

A kasar China, an Cafke wasu mutane mabiya wata darikar Addnin Kirista su fiye da dubu, da ke yada jita jitar karshen Duniya ya zo, tare da kalubalantar jama’iyyar Kwaminisanci mai mulkin kasar.

Mutum Mutumin da aka yi wa kwalliya domin kawata bukin Kirsimeti a kasar China
Mutum Mutumin da aka yi wa kwalliya domin kawata bukin Kirsimeti a kasar China REUTERS/Stringer
Talla

‘Yan kungiyar da ake kira ALMIGHTY GOD a Turance, sun ce gobe juma’a za a shiga cikin duhun da zai kawo karshen duniya, don haka suka nemi a kifar da gwamnatin kwaminist mai mulkin kasar China, da suke kira babban dodo.

Mabiya akidar sun ce an shiga wani sabon zamanin da aka samu Mace a matsayin Yesu, da ke jagorancin duniya, suna masu cewa ambaliyar ruwa irin ta tsunami, da girgizar kasa za su mamaye duniya.

Kafafen yada labarun kasar ta China sun ruwaito ‘Yan kungiyar suna amfani da jima’I wajen yada manufofinsu, inda suke kira ga mata mabiyansu su rinka yin amfani da jikinsu, domin jan hankulan mazajen da ba su da aure.

Kungiyar kuma tana yada manufofinta ne cikin sirri, inda membobinta ke amfani da wasu sunaye kamar “Dan Zomo” ko “Dan Kare”, don boye kansu daga sauran mutane, kuma ba su amfani da wayar hannu ko sauran na’urorin sadarwa.

Jama’iyyar Kwaminist dai a kasar China an dade tana karya duk wata kafa da za’a kalubalance ta, don haka ne ta ke rugurguza duk wata kungiyar addinin da ta nemi bijirewa, kamar yadda ta yi wa kungiyar Falun Gong, a shekarar 1990 da ta ba hukumomin kasar mamaki, bayan da ta tara dubun dubatar masu zanga-zanga cikin sirri a muhimman wurare daba-daban, da suka hada da dandalin Tiananmen, na birnin Beijing.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.