Isa ga babban shafi
China/Sin

Wata ‘Yar Tibet ta cinnawa kanta wuta a kasar China

Wata yarinya ‘Yar shekara 16 ta cinnawa kanta wuta a yankin Tibet a yayin da dangantaka tsakanin 'Yan Tibet da gwamnatin kasar Sin a yankin ke kara tsamari. Lamarin ya auku ne a kauyen Dageri dake Arewa maso Yammacin yankin Qinghai, wanda yanki ne dake da yawan ‘Yan Tibet.  

Wasu 'Yan Tibet a kasar China
Wasu 'Yan Tibet a kasar China REUTERS/Navesh Chitrakar (NEPAL
Talla

Rahotanni sun nuna cewa an lillibe gawarta an aikawa da iyalanta.

Akalla mutane 90 suka mutu ta hanyar cinnawa kansu wuta a yankin na Tibet tun daga shekarar 2009, domin nuna rashin yadda da mulkin mallaka da China ke wa ‘Yan yankin.

Mafi akasarin wadanda sukan cinnawa kansu wuta na mutuwa, a yayin da wannan yarinya itace mafi kankantar shekaru a cikin wadanda kan yi hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.